Wani shiri na koyar da ilimin na’ura mai kwakwalwa kyauta da ƙungiyar Garkuwar Matasa Foundation ta gudanar a ƙaramar hukumar Gwarzo ta kammala, inda matasa 227 daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar suka amfana.
Shugaban ƙungiyar, Bashir Garba Sardauna Getso, ya bayyana cewa an kammala shirin ne a ranar Lahadi, 1 ga Nuwamba, 2026, yana mai cewa hakan na cikin ƙoƙarin samar wa matasa ilimin fasahar zamani.
Ya kuma bayyana farin cikinsa bisa kammala shirin, tare da godiya ga iyaye, malamai, sarakuna da sauran waɗanda suka taimaka wajen ganin an cimma wannan buri.
