Rikici ya ɓarke a jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, bayan da jami’ai biyu suka bayyana sakamako daban-daban na zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa gabanin zaɓen 2027.
A sakamakon farko da shugaban kwamitin zaɓen, Dakta Auwal Abdullahi Aliyu, ya sanar a Gusau ranar Litinin, Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya samu ƙuri’u 49,176, yayin da Tijjani Yahaya Kaura ya samu 9,628.
Sai dai wani jami’in zaɓen ya bayyana Tijjani Yahaya Kaura a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’u 16,758, yayin da Sahabi Ya’u ya samu 1,465.
Zaɓen ya gudana ne bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Sokoto ta tabbatar da hukuncin soke zaɓen fidda gwani na farko, sakamakon ƙarar da Sani Abdullahi Shinkafi ya shigar.
Rahotanni sun ce an samu tashin hankali yayin zaɓen, yayin da sakamakon biyu masu cin karo da juna suka haifar da rashin tabbas kan wanda zai wakilci APC a zaɓen Sanatan Zamfara ta Arewa na 2027.
