Wasu ƴan bindiga sun kashe jami’an ƴansanda biyar a wani harin kwanton ɓauna da suka kai wa ayarin motocin jami’an tsaro a kan hanyar Sokoto zuwa Gusau, a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce jami’an na kan hanyarsu daga Sokoto zuwa Zamfara domin gudanar da wani aiki na musamman lokacin da maharan suka buɗe musu wuta.
Wani jami’in ɗansanda da ya tsira daga harin ya bayyana cewa suna tafiya ne cikin motoci uku, lokacin da ƴan bindigar suka kai hari kan motar da ke ƙarshen ayarin.
Kakakin ofishin Mataimakin Sufeto-Janar na Ƴansanda mai kula da shiyya ta 10 a Sokoto, Abdullahi Faruk, ya tabbatar da mutuwar jami’an biyar.
Ya ce an kai gawarwakinsu ɗakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto.
Rahotanni sun kuma nuna cewa jami’an na kan hanyarsu ta zuwa aikin samar da tsaro a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa.
