Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta ƙalubalanci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya gabatar da hujjojin da ke nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na da hannu a shari’ar da ta shafi takarar Aminu Abdussalam Gwarzo, ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).
APC ta bayyana zargin Kwankwaso a matsayin wanda ba shi da tushe, tana mai zargin tsohon gwamnan da ƙoƙarin ɓata mata suna da kuma matsa mata lamba gabanin zaɓen gwamna na 2027.
Kwankwaso dai ya zargi Gwamna Abba da jam’iyyar APC da hannu wajen ƙoƙarin hana Gwarzo tsayawa takara, bayan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ’yan takara ba tare da sunansa ba.
Sai dai shugaban APC na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya musanta zargin, yana mai cewa babu jam’iyyar APC ko gwamnatin jihar Kano da ke da hannu a shari’ar.
Doguwa ya ce rikicin ya samo asali ne daga cikin gida na jam’iyyar NDC, inda wasu mambobinta suka shigar da ƙara a kan jam’iyyar kanta, ba APC ko gwamnatin Kano ba.
Ya ce:
“Shari’ar da ake magana a kai ta samo asali ne daga rikicin cikin gida na jam’iyyar NDC. Wasu daga cikin mambobinta ne suka shigar da ƙara a kan jam’iyyar, ba APC ko gwamnatin jihar Kano ba.”
Shugaban APC ɗin ya zargi Kwankwaso da ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin cikin gida da jam’iyyarsa ke fuskanta, ta hanyar jawo APC da Gwamna Abba cikin rikicin.
Ya kuma ƙalubalanci Kwankwaso da ya gabatar da sahihan hujjoji da za su tabbatar da zargin cewa APC ko Gwamna Abba sun ɗauki nauyin shari’ar ko kuma sun yi tasiri a kanta.
APC ta jaddada cewa ɓangaren shari’a na da ’yancin gudanar da aikinsa bisa kundin tsarin mulki, ba tare da katsalandan daga jam’iyya ko gwamnati ba.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ’yan siyasa da su bar hukumomin da abin ya shafa su gudanar da ayyukansu bisa doka, maimakon mayar da rikicin cikin gida na jam’iyya zuwa rikicin siyasa.
Ta ce duk wani ɗan takara da ya cika sharuddan doka yana da ’yancin shiga zaɓen 2027.
APC ta buƙaci al’ummar Kano da su yi watsi da zarge-zargen da ke danganta jam’iyyar da Gwamna Abba da shari’ar da ta shafi takarar Gwarzo, tana mai cewa ba su da hannu kai tsaye ko a fakaice a cikin shari’ar.
