Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Tenerife, Jesús de Miguel, ya rasu yana da shekaru 30 bayan samun munanan raunuka sakamakon karo da mai tsaron ragar ƙungiyar Andorra, Jesús Owono, a yayin wasan da suka fafata a daren Litinin.
Lamarin ya faru ne lokacin da Owono ya fito daga ragar tasa domin ƙoƙarin tare ƙwallon da aka aika daga nesa, inda ya yi karo da De Miguel, gwiwarsa ta bugi ƙirjin ɗan wasan Tenerife.
Shaidun gani da ido sun ce De Miguel ya faɗi ƙasa nan take cikin raɗaɗi, kafin daga bisani ya daina motsi. ’Yan wasan ƙungiyoyin biyu sun yi gaggawar kiran jami’an lafiya domin kai masa ɗauki.
Alkalin wasan ya bai wa Owono jan kati saboda karon, sannan aka dakatar da wasan .
Da farko, Tenerife ta fitar da sanarwar cewa De Miguel na samun sauki bayan an kai shi asibiti. Sai dai daga baya ƙungiyar ta bayyana cewa yanayin lafiyarsa, musamman na kwakwalwa, ya tabarbare.
A safiyar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, ƙungiyar ta tabbatar da rasuwarsa da ƙarfe 8:00 na safe.
A cikin sanarwar ta, ƙungiyar Tenerife ta ce:
“Cikin tsananin baƙin ciki, zuciyarmu cike da alhini, kuma har yanzu ba mu iya gaskata abin da ya faru ba, ƙungiyar CD Tenerife na sanar da rasuwar Jesús de Miguel Alameda a safiyar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, da ƙarfe 8:00 na safe.”
Ƙungiyar ta ce babu wani abu da zai iya rage radadin wannan babban rashi, tare da miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa, abokan wasansa da sauran masu ruwa da tsaki a ƙungiyar.
Ta kuma bayyana cewa iyalan marigayin sun gode wa duk waɗanda suka aika saƙonnin ta’aziyya da goyon baya, amma sun nemi a ba su damar zaman makoki cikin sirri.
Ita ma ƙungiyar Andorra ta wallafa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin da ƙungiyar Tenerife.
Tsohon ɗan wasan Barcelona, kuma shugaban ƙungiyar Andorra, Gerard Piqué, ya nuna alhininsa kan rasuwar, inda ya rubuta a shafinsa na X cewa:
“Na yi matuƙar baƙin ciki.”
