Hukumar kare haƙƙin masu sayayya ta jihar Kano, KCPC, ta rufe wasu shaguna a kasuwar Singer tare da kama wasu ’yan kasuwa bisa zargin sauya ranar ƙarewar amfani da madarar gari da ta riga ta lalace domin sake sayar da ita.
Hukumar ta gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar shugabannin kasuwar, bayan samun bayanan sirri daga ƙungiyar ’yan kasuwar.
Ana zargin waɗanda aka kama da sauya bayanan ranar ƙarewar amfanin madarar domin yaudarar masu sayayya su sayi kayan da wa’adin amfaninsu ya ƙare.
