Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniMagoya bayan Pillars na bukatar a dauki Usman Abdallah sabon mai horarwa

Magoya bayan Pillars na bukatar a dauki Usman Abdallah sabon mai horarwa

Date:

Yayin da ake shirye-shirye fara sabuwar kakar Wasannin shekarar 2022/2023 wasu magoya bayan Kano Pillars na bukatar kungiyar ta dauki Usman Abdallah a matsayin sabon mai horarwa a tawagar.

 

Kano Pillars kawo yanzu na karkashin jagoranci Salisu Yusuf D Balack da Ibrahim A Musa a matsayin masu horar da kungiyar, sai dai kungiyar ta bukaci su sake neman aikin horarwa a tawagar.

 

Kuma Kungiyar ta Sai Masu Gida ta fada gasar kwararru ta kasa, bayan gaza ci gaba da samun damar buga gasar NFPL a kakar wasanni mai kamawa.

 

Shi dai Usman Abdallah dan asalin jihar Kano ne, wanda ya fara aikin horarwa tun daga kasar Faransa.

 

Kana daga baya ya dawo Najeriya ya horar da karamar kungiyar Kano Pillars, sannan ya jagoranci Enyimba har ya lashe gasar NPFL a kungiyar.

 

Haka zalika ya horar da kungiyar Wikki Tourist ta jihar Bauchi, kuma a yanzu yana horar da Katsina United.

 

Amma a wata hira da Premier Radio Usman Abdallah ya ce lokaci ne kadai zai yanke hukunci ko zai zo kungiyar ko aka sin haka.

 

“Ni bani da matsala da kowa, yanzu ina aikin horar da Katsina, amma idan Pillars suka nai meni zanzo domin kuwa Kano gida nane” a cewar Usman Abdallah.

 

Ya kuma kara da cewa tuni hankalinsa ya karkata ga shirin tun karar sabuwar kakar wasanni mai kamawa.

 

A gefe guda munyi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun Kano Pillars Rilwanu Idris Malikawa Garu sai dai bamu samu ji daga gare shi ba sakamakon ayyyuka da suka sha kansa.

Latest stories

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...