Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniBarcelona ta fice daga gasar cin kofin zakarun turai

Barcelona ta fice daga gasar cin kofin zakarun turai

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fice daga gasar cin kofin zakarun turai UEFA Champions, bayan rashin nasara a hannun Bayern Munici da ci 3_0.

 

Wasan dai ya gudana a wannan rana ta Laraba, a filin wasa na Spotify Camp Nou da ke kasar Sifaniya.

 

Dan wasa Sadio Mane ne ya fara zura kwallon farko a minti na 10 da wasan, bayan samun taimako daga hannun dan wasa Serge Gnabry.

 

Sai dai kuma dan wasa Eric Maxim Choupo-Moting ya kara kwallo ta biyu a minti na 35, bayan da ya samu taimako daga Serge Gnabry.

 

Shima dan wasa Benjamin Pavard ya zura kwallo ta uku a minti na 95 bayan karin lokaci da alkalin wasa yayi.

 

Amma wasan an kammala 3-0 tsakanin kungiyoyin guda biyu, wato Barcelona da kuma Bayern Munich.

 

Yanzu haka dai Barcelona ta fice daga gasar cin kofin zakarun turai ta kakar wasannin shekarar 2022/2023.

 

Wanda kawo yanzu tana da maki 4 a wasanni biyar da ta buga a rukunin B na gasar.

 

Kawo yanzu kungiyar Barcelona ko tayi nasara a wasan karshe na rukunin B da zata kece raini da Viktoria Plzen a ranar 1 ga Nuwambar da muke ciki, to Kungiyar ba zata ci gaba da buga gasar ba.

 

Inda a yanzu ta tabbata Barcelona ta koma gasar Europa League mai daraja ta biyu ta nahiyar turai.

 

Rukunin B dai Bayern Munich ce a mataki na farko da maki 15 bayan buga wasa biyar.

 

Sai kuma Inter Milan tana mataki na biyu da maki 10 a wasa biyar din da ta fafata.

 

Haka kuma Barcelona tana mataki na uku da maki hudu, yayin da Viktoria Plzen ta ke a mataki na karshe a rukunin kuma ba tada maki ko daya.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories