Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMa'aikatar lafiya ta Hamas ta ce an kashe Falasɗinawa 34,789 a yankin...

Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce an kashe Falasɗinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba.

Date:

Daga ketare, Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba, bayan da Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙinta na soji a matsayin martani ga hare-haren Hamas a kudancin Isra’ila.

Adadin waɗanda suka mutu ya haɗa da aƙalla mutane 54 da suka mutu a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji ma’aikatar.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta kuma ce Falasdinawa 78,204 ne suka jikkata tun ranar 7 ga watan Oktoba, yayin da yaƙin ya shiga wata na takwas.

A ranar 7 ga watan Oktoba ne ‘yan bindigar Hamas suka kai hari a kudancin Isra’ila, inda suka kashe mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da fiye da mutum 250.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...