
Ishaq Sani Dambazau
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na facebook, Kwankwaso ya ce bayan tsawon lokacin da ya shafe yana hidimtawa ƙasa, marigayi Rabe Abubakar bai cancanci samun wannan sakamakon ba sai dai rasuwarsa ta zo cikin yanayi mai tayar da hankali.
Ya bayyana cewa rasuwar tsohon sojin na nuni da yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a Najeriya, yana mai cewa yawaitar rasa jami’an tsaro masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, tare da sauran ‘yan Najeriya a hannun ‘yan ta’adda, abu ne da bai kamata a ɗauke shi da wasa ba.
Kwankwaso ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da ceto matar marigayin da sauran mutanen da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane cikin gaggawa da kuma lafiya.
Daga bisani, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai, abokai da sauran ƴan kasa baki ɗaya bisa rasuwar marigayi Janar Rabe Abubakar.
