Saurari premier Radio
37.8 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKungiyar Kwadago NLC Ta Bukaci Gwamnati Da CBN Su Gaggwata Kawo Karshen...

Kungiyar Kwadago NLC Ta Bukaci Gwamnati Da CBN Su Gaggwata Kawo Karshen Karancin Takardun Kudi Na Naira

Date:

Kungiyar kwadago ta NLC ta bukaci gwamnatin tarayya da babban bankin kasa CBN, su yi gaggawar samar da mafita kan karancin takardun kudi na Naira da al’umma ke fama da shi a halin yanzu.

Shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce hakurin yan Najeriya ya kusa karewa kan uzurin da gwamnati ke cewa ya kamata a yi mata.

Ya ce duk da cewa gwamnati da babban bankin CBN sun fito karara sun nuna cewa ba da gangan aka samu wannan matsala ba, amma hakan abin kunya ne ace gwamnati ta gaza shawo kan matsalar da ake ganin tana barazana ga tattalin arziki musamman ga masu karamin karfi.

Ya kara da cewa babu wata gwamnati idan har ta amsa sunan mai kishin al’umma da za ta nade hannu tana kallon halin kuncin da suke ciki.

NLC ta kuma bayyana damuwa kan halin da yan Najeriya suka tsinci kansu, musamman a dai-dai lokacin da ake shirye-shirye bukukuwan Kirismeti da na sabuwar shekara.

Ajaero, ya ce idan har abinda CBN ya bayyana cewa, masu hannu da shuni ne ke kwashe takardun Naira suna boyewa a gidajensu domin kaucewa bincike, to yakin da gwamnati ke yi da cin hanci da rashawa na cike da kura-kurai.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...