Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki martanin da gwamnatin tarayya ta mayar kan sace ɗalibai da malamai a jihar Oyo, yana mai kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali wajen ceto su maimakon raba kayan tallafi ga iyalansu.
Atiku ya bayyana lamarin a matsayin wata alama ta yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya, yana mai cewa rashin tsaro a ƙarƙashin gwamnatin yanzu ya zama kamar wani abu na yau da kullum maimakon a ɗauke shi a matsayin matsalar gaggawa.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Laraba, Atiku ya nuna damuwarsa kan rahotannin da ke cewa jami’an gwamnati sun kai buhunan shinkafa da sauran kayan tallafi ga iyalan waɗanda aka sace.
Ya ce irin wannan mataki na nuna rashin tausayi da kuma gazawar shugabanci a lokacin da iyalai ke jiran a dawo musu da ’ya’yansu cikin koshin lafiya.
Ya ƙara da cewa iyayen da ba su san halin da yayansu ke ciki ba ko suna cikin yunwa, rashin lafiya, firgici ko ma suna raye, ba kayan tallafi suke bukata ba, illa a tabbatar an kuɓutar da su.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa abin da iyalan ke bukata shi ne ɗaukar mataki cikin gaggawa, jagoranci mai ƙarfi da kuma tsari na tsaro da zai tabbatar da ceto ɗaliban da malamai da aka yi garkuwa da su.
Atiku ya kuma zargi gwamnati da dogaro da dabarun yaɗa labarai maimakon samar da mafita ga matsalolin tsaro, yana mai cewa har yanzu miyagu na ci gaba da aikata laifuka yayin da jama’a marasa laifi ke ci gaba da shan wahala.
