Jigo a jam’iyyar PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus kafin zaɓen shekarar 2027, saboda yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a Najeriya.
Yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News, Baba-Ahmed ya buƙaci yan Najeriya su ƙi zaɓen Tinubu a zaɓen 2027 saboda yadda ya gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya.
Ya ce: “A bayyane yake cewa Tinubu ya kasa shawo kan rashin tsaro da ke ƙara kamari. Kafofin watsa labarai, Majalisar Dokoki da ƙungiyoyin farar hula sun faɗi duk abin da ya kamata a faɗa, amma Tinubu da magoya bayansa suna nuna kamar matsalar ce da za a iya rayuwa da ita.”
Ya ƙara da cewa hare-hare da garkuwa da yara suna ci gaba da faruwa a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ya sa kusan ko’ina a Najeriya ya zama mai fuskantar barazanar tsaro.
A cewarsa: “A ƙasa mai bin tsarin dimokuraɗiyya da ci gaba, irin tarihin Tinubu kan rashin tsaro da tuni ya sa ya rasa kujerarsa. Har yanzu ba a makara ba a ce ya kamata ya yi murabus.”
Baba-Ahmed ya ce idan aka duba yadda gwamnati ke tafiyar da harkokin tsaro zuwa lokacin zaɓe, babu buƙatar jira domin ’yan Najeriya za su iya nuna rashin amincewarsu da shi ta hanyar zaɓe.
Ya kuma jaddada cewa kiransa na Tinubu ya yi murabus ba ya da alaƙa da siyasa ko adawa.
