Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta dakatar da wani likita da ke aiki a daya daga cikin manyan asibitoci mallakin gwamnati kan zargin zuwa aiki cikin maye da kuma aikata halayen da suka saba da ka’idojin aiki.
Wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar, Samira Sulaiman, ta sanyawa hannu, ta bayyana halayen a matsayin abinda ba za a lamunta ba saboda sun saba da ka’idoji da dokokin aikin likitanci.
Ta ce sakataren zartarwa na hukumar, Dr. Mansur Mudi Nagoda, ya amince da aikewa da likitan takardar tambaya tare da dakatar da shi daga aiki har sai an kammala cikakken bincike.
Ya ce binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da samun rashin da’a akan likitan, lamarin da ya sa aka dauki matakin ladabtarwa cikin gaggawa.
Sanarwar ta jaddada cewa bayar da kulawar lafiya na bukatar cikakkiyar kwarewa, ladabi da kuma kyakkyawan tunani, musamman a manyan a asibitoci mataki inda rayukan marasa lafiya ke hannun ma’aikatan lafiya.
Dr. Nagoda ya kuma yi gargadin cewa duk wani aiki da zai iya kawo nakasu ga amincewar jama’a da tsarin kiwon lafiya zai fuskanci hukunci mai tsauri.
