Jihar Kano za ta karbi bakuncin gasar tseren takalmin taya karo na farko a Najeriya (1st Edition of Kano Roller Skates), wadda za ta hada mahalarta daga jihohi 26 na kasar nan.
Za a gudanar da gasar daga ranar 28 zuwa 30 ga Oktoba, 2026, a filin Mahaha Sport Complex, Kofar Naisa, Kano.
Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tukur Babangida, tare da Mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin wasanni, Alhaji Sani Danja, da sauran manyan baki ne za su jagoranci bude wannan gasa.
Da yake bayyana muhimmancin gasar, Shugaban kungiyar masu tseren takalmin taya ta Kano, Ibrahim Aliyu Khalid, ya ce wannan ita ce gasa ta farko irinta da aka fara shirya wa a fadin Najeriya.
Ya bayyana cewa wannan nasara ta samu ne sakamakon goyon baya da kokarin Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano wajen bunkasa sabbin wasanni da samar da dama ga matasa domin bayyana hazakarsu.
Hukumar Wasanni ta Jihar Kano na ci gaba da daukar matakai wajen bunkasa dukkanin nau’ikan wasanni tare da samar da yanayi mai kyau ga ‘yan wasa domin samun ci gaba a matakin kasa da kasa.
