Tsohon sakataren kwamitin Amintattu na jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya ce akwai wani sabon sauyi na siyasa da ke tafe, inda ya bayyana cewa manyan ‘yan adawa ciki har da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, da takwaransa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, za su sanar da wani sabon sauyin siyasa a ranar Litinin din nan.
Galadima ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ƙungiyar Obi-Kwankwaso Movement ta shirya a birnin tarayyar Abuja, yayin da ake fuskantar rashin tabbas kan makomar haɗin kan jam’iyyar adawa kafin zaɓen 2027.
Jarida Punch ta rawaito cewa, har kawo zuwa wannan lokacin ba a ambaci sunan sabuwar jam’iyyar ba, majiyoyin kusa da tsofaffin gwamnonin sun bayyana cewa suna dab da kammala shirye-shiryen shiga wata sabuwar jam’iyya ta NDC wacce ake dangantawa da tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson.
Ana ganin wannan mataki na zuwa ne bayan makonni na jita-jita game da inda Obi da Kwankwaso za su dosa a siyasa, musamman bayan hukuncin kotun ƙoli da suka shafi jam’iyyun adawa.
