Mai Martaba Sarkin Katsina, Dokta Abdulmuminu Kabir, ya naɗa sabbin hakimai uku da gwamnatin jihar ta amince da ƙirƙirowa daga cikin masarautar.
A ranar Asabar 2 ga watan Mayu na 2026 aka naɗa ƙarin harin hakiman uku, wanda ya akai yawan hakiman masarautar zuwa 50, kamar yadda Sarkin Labaran masarautar, Alhaji Ibrahim Yaro ya tabbatar wa wakilinmu.
Sabbin hakiman da aka naɗa su ne, Ahmad Abdulmuminu Kabir wanda yake ɗa ne ga Sarkin Katsina a matsayin, Ɗanmajen Katsina Hakimin Dankama.
Ita wannan kujera ta hikimcin garin Dankama ba baƙuwa ba ce a tarihi tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, a lokacin Ƙaura Amah.
Daga baya ne aka mayar da ita ƙarƙashin mulkin Sarkin Sulluɓawan Katsina, Hakimin Kaita.
Kazalika, an naɗa babban ɗan Gwamna Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, wato, Muhammadu Dikko Raɗɗa a matsayin Gwagwaren Katsina, Hakimin Raɗɗa.
Kafin naɗin nashi, mahaifinsa, Gwamna Raɗɗa ke riƙe da wannan muƙamin na Gwagware wanda yake ɗaya daga cikin ’yan Majalisar Sarki, masu taimakawa masarauta a ayyuka na musamman.
Bayan ƙirƙiro da sabbin hakimai ne a masarautar, wannan muƙamin Gwagware ta koma a matsayin hakimci, sannan shi ne Gwamna Raɗɗa ya janye ya bai wa ɗan nasa wannan matsayi.
