Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJami'ar Yusuf Maitama Sule tayi sabon shugaban kungiyar dalibai.

Jami’ar Yusuf Maitama Sule tayi sabon shugaban kungiyar dalibai.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

Sabon shugaban kungiyar daliban Jami’ar Yusuf Maitama Sule Tafida Akilu ya ce zasu yi kokari wajen tsaftace siyasar dalibai tare da gyara alakar dake tsakanin malamai da dalibai.

Tafida Akilu ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar sa da Premier Radio bayan ya zama shugaban daliban jami’ar.

Tafida Akilu ya ce a wannan karon ba a gudanar da zabe ba yayin samar da shugabbannin daliban kasancewar hukumar jami’ar ta yi maslaha a tsakanin ‘yan takara, wanda hakan ya ba shi damar kasancewa shugaban kungiyar.

Ya kara da cewa zasu fito da sabbin tsare-tsare wajen ganin sun taimakawa dalibai ta bangaren koyo da koyarwa.

Sabon shugaban kungiyar daliban Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Tafida Akilu ya bukaci dalibai su bashi hadin kai domin gudanar da shugabanci cikin nasara.

Latest stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...

Related stories