35.9 C
Kano
Monday, March 20, 2023
HomeLabaraiJami’ar Bayero Ta Musanta Kara Kudin Makaranta Ga Dalibai.

Jami’ar Bayero Ta Musanta Kara Kudin Makaranta Ga Dalibai.

Date:

Related stories

Muna cigaba da tattara bayanai game da gobarar kasuwar kurmi – SEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano ta...

APC ta shirya lauyoyinta domin tunkarar PDP da LP a kotu

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC...

Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero Kano ta musanta labarin cewa ta kara kudin makaranta ga dalibanta da kuma wadanda ke son shiga.

 

Cikin wani sautin murya da mai magana da yawun Jami’ar, Malam Lamara Garba, ya aikowa Premier radio, yace labarin ba gaskiya bane, don haka ya bukaci iyayen dalibai, da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankulansu.

 

Ya kara da cewa har yanzu jami’ar bata samar da matsaya ba, kan kudin da ya kamata dalibai su biya a bana.

 

Tuni dai wasu jami’o’i musamman na gwamnatin tarayya ke ci gaba da kara kudin makaranta ga dalibai, wanda hakan ya haifar da damuwa ga daliban da iyayensu.

Latest stories