Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu, ya ce rundunar ’yan sandan ƙasar ba ta da wata manufa ta siyasa a zaɓen gwamnan Jihar Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
Tunji Disu ya ce ’yan sanda za su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa, rashin nuna bambanci da kuma bin doka kafin zaɓen, lokacin gudanar da shi da kuma bayan kammalarsa.
Ya jaddada cewa rundunar ba za ta goyi bayan wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara ba, yana mai cewa babban burinta shi ne tabbatar da zaman lafiya da tsaro domin jama’a su gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Kalaman Sufeto-Janar na ’Yan Sandan sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar fargaba gabanin zaɓen Osun, inda ake sa ran jami’an tsaro za su taka muhimmiyar rawa wajen kare masu kaɗa ƙuri’a da kayayyakin zaɓe.
Rundunar ’yan sandan ta ce za ta tabbatar da cewa doka ta yi aiki tare da samar da ingantaccen yanayi da zai ba ’yan ƙasa damar gudanar da zaɓensu cikin lumana.
