By Khadija Isma’il Ahmad
Hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Kano ta nemi haɗin kan al’umma, musamman iyaye da masu ruwa da tsaki, domin samun nasarar shirin rigakafin yara da za a gudanar a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Mataimakin jami’in kula da rigakafi na hukumar, Muhammad Hassan Danbappa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar. Ya jaddada muhimmancin haɗin kai daga iyaye da shugabannin al’umma domin tabbatar da cewa dukkan yara sun amfana da wannan shiri.
Danbappa ya ƙara da cewa, za a fara gudanar da rigakafin ne a ranar da aka tsara, inda jami’an lafiya za su zagaya gidaje da wuraren taruwar jama’a domin yi wa yara allurar rigakafin cututtuka masu haɗari.
Ya kuma bukaci iyaye da su fito da ‘ya’yansu domin karɓar rigakafin, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kare lafiyar yara da kuma hana yaduwar cututtuka a cikin al’umma.
