Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da daukar jami’an tsaro masu kula da gandun daji dubu daya a jihar Katsina domin taimakawa yaki da yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ne ya sanar da hakan bayan wani taro da malamai da sauran masu ruwa da tsaki suka gudanar a gidan gwamnati.
Gwamnan ya ce sabbin jami’an za su samu horo da kayan aiki domin kula da dazuka da yankunan karkara da masu aikata laifuka ke amfani da su a matsayin maboyarsu.
Ya kara da cewa nasarar yaki da rashin tsaro ba za ta samu ba sai da hadin kan al’umma da hukumomin tsaro.
