Gwamnatin Kano ta bukaci asibitocin dabbobi da masu sana’arJima, da su rungumi tsarin zamani musamman yin amfani da na’ura mai kwakwalwa wajen ajiyar muhimman bayanai don gudun salwantar su.
Kwamshinan Ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi na Kano Dr Aliyu Isa Aliyu, shi ne ya bukaci hakan lokacin da ya kai ziyarar aiki wasu daga cikin asibitocin dabbobi da kamfanonin jima na jihar Kano.
A cewar Dr Aliyu yin amfani da na’ura mai kwakwalwa domin ajiyar bayanai, ita ce kadai hanyar da asibitocin zasu iya ajiye kididdiga da bin diddigin dukkan matsalolin da cututtukan dabbobin da suka taba fuskanta.
Da yake jawabi a madadin asibitoci da kamfanin Jimar da aka ziyarta Bashir Garzali El Mahmud ya yabawa gwama Abba Kabir Yusuf bisa hangen nesan da yayi wajen bawa Dr Aliyu Isa Aliyu Shugabacin ma’aikatar ta bunkasa kiwon dabbobi la’akari da kwarewa da jajircewar da yake da ita akan ayyukan sa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa daga cikin asibitocin da kwamishinan ya ziyarta akwai asibitin kula da lafiyar dabbobi na Gwale da na Kundila, inda Dr Aliyu ya basu tabbacin cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da bunƙasa ayyuka da kula da hakkokin su.
