Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Musulman Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 Hijira.
A cikin saƙon da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya ce darussan Hijira kamar sadaukarwa, haƙuri, sabuntawa da kuma dogaro ga Allah na da matuƙar muhimmanci wajen gina ƙasa mai zaman lafiya da ci gaba.
Tinubu ya kuma yi kira ga yan Najeriya, musamman Musulmi, da su rungumi kyawawan halaye kamar gaskiya, haƙuri, juriya da kishin ƙasa domin ƙarfafa haɗin kai da ci gaban Najeriya.
Ya yi addu’ar Allah ya sanya sabuwar shekarar ta kasance mai albarka, zaman lafiya da wadata ga al’ummar ƙasar.
