Gwamnatin jihar Katsina ta ce wani tsohon hadimin gwamnati mai suna Nura Aliyu Garwa, wanda ake zargi da jagorantar wata kungiyar masu garkuwa da mutane, tuni an dakatar da shi daga mukaminsa kafin ya nemi takarar kujerar majalisar dokokin jihar.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar, gwamnatin ta ce an dakatar da Garwa ne daga mukaminsa na babban mataimaki na musamman kan ci gaban al’umma saboda zargin karkatar da kayayyakin tallafi da aka ware domin rabawa al’ummomi a karamar hukumar Batsari.
Sanarwar ta kara da cewa daga baya Garwa ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar mazabar Batsari a majalisar dokokin jihar Katsina.
Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, musamman ganin cewa ana zargin mutum mai irin wannan matsayi da hannu a satar wani yaro dan shekara takwas a cikin birnin Katsina.
Ya yaba wa hukumomin tsaro saboda kokarinsu na yaki da matsalar tsaro da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Gwamnan ya kuma bukaci al’umma su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi.
A baya-bayan nan ne rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta gabatar da wasu da ake zargi da hannu a kungiyar masu garkuwa da mutanen da ake alakanta da sace wani karamin yaro a unguwar Sardauna Estate da ke cikin birnin Katsina.
