Gwamnatin Kano ta sake tabbatar da aniyar ta na ganin kowane yaro a jihar ya samu damar ilimi mai inganci, kiwon lafiya ingantacce da yin rayuwa cikin walwala ba tare da la’akari da jinsi, nakasa, addini, ƙabila ko matsayin tattalin arziki ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin bikin ranar Yara ta Duniya ta shekarar 2026 da aka gudanar a dakin taro na Coronation Hall dake fadar gwamnatin Kano.
Gwamna Abba wanda mataimakinsa Murtala Sule Garo ya wakilta, ya ce taken bikin na bana ya jaddada muhimmancin samarwa yara dama, kulawa, kariya da ilimi domin gina kyakkyawar makomar Najeriya.
Gwamnan ya ce yara su ne ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa kuma su ne shugabannin gobe, saboda haka gwamnatin Kano za ta ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari a baya.
Mataimakin gwamnan ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da zuba jari a fannin ilimi, ƙarfafa tsarin kare haƙƙin yara, inganta harkokin kiwon lafiya da samar da yanayi mai kyau da zai baiwa yara damar bunƙasa baiwarsu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwamishiniyar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman, Hajiya Amina S. Abdullahi na yin kira ga Gwamna Abba da ya ƙaddamar da Kwamitin Kare Haƙƙin Yara na Kano domin tabbatar da aiwatar da Dokar Kare Haƙƙin Yara yadda ya kamata.
