Gwamnatin Kano ta rufe wasu kwalejojin koyar da Harkokin kiwon lafiya guda biyu masu zaman kansu bisa zargin su da yin aiki ba tare da cika ka’idojin da doka ta tanada ba a karamar hukumar Nasarawa.
Ma’aikatar Lafiya ta jihar ce ta bayyana hakan bayan gudanar da bincike da tantancewa kan cibiyoyin, inda aka gano cewa ba su cika sharuddan da ake bukata ba wajen kafawa da gudanar da makarantu.
Da yake yiwa Premier radio karin bayani, jami’in yada labaran ma’aikatar Nabulisi Abubakar K/Na’isa ya ce Kwalejojin da abin ya shafa sun hada da IBN SINA College of Health Science and Technology da ke Dakata Kawaji, da Life Line College of Health Science and Technology da ke yankin Dakata Industrial Area.
A cewar Ma’aikatar Lafiyar, cibiyoyin biyu na gudanar da ayyukansu ba tare da sahalewar ma’aikatar ba, haka kuma ba su da amincewa daga hukumomi da kwamitocin da ke kula da ilimin lafiya da horas da ma’aikatan lafiya a Najeriya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Nabulisi na cewa binciken da aka gudanar ya kuma gano karancin kwararrun malamai, rashin ingantattun kayan koyarwa da gine-ginen da suka dace, tare da gazawa wajen bin ka’idojin ilimi da gudanarwa da ake bukata domin samar da kwararrun ma’aikatan lafiya.
