Gwamnatin Kano ta dakatar da Manajan Cibiyar Samar da Ruwa ta Thomas bayan gano munanan ayyukan barna da satar kayayyakin gwamnati a cibiyar.
Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Muhalli ta Jihar, Dr Dahiru M Hashim ne ya sanar da hakan yayin wata ziyarar duba ayyukan gyaran cibiyoyin samar da ruwa a Kano.
Dr Hashim ya ce binciken da suka gudanar a cibiyar ta Thomas da ke yankin Danbatta ya nuna cewa cibiyar ta daina aiki kusan shekaru uku da suka gabata, lamarin da ya janyo matsalar samar da ruwa ga kananan hukumomi uku da cibiyar ke kula da su.
Ya bayyana cewa binciken ya gano sace-sacen wayoyin lantarki da sauran muhimman kayan aiki na cibiyar, har ma da lalata wani sabon aikin lantarki da aka kammala watanni uku da suka gabata kafin a fara amfani da shi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Kwamishinan ya kuma zargi jami’an tsaron da aka dorawa alhakin kare cibiyar da mayar da harabar wajen noma amfanin gona, maimakon kula da kadarorin gwamnati, wanda sakamakon hakan, gwamnati ta dakatar da manajan cibiyar tare da fara gudanar da cikakken bincike, domin daukar matakin shari’a idan aka samu wadanda ke da hannu a aikata laifukan.
