Rahotanni sun nuna cewa kudin da Najeriya ke kashewa wajen shigo da man fetur daga kasashen waje ya ragu matuka, daga kusan naira tiriliyan 2.3 a zangon farko na shekarar 2025 zuwa kasa da naira biliyan 90 a zangon farko na shekarar 2026. Wannan na nufin an samu raguwar sama da kashi 96 cikin 100 cikin shekara guda.
Bayanan da aka fitar sun nuna cewa an kashe kimanin naira biliyan 87.4 ne kawai wajen shigo da fetur a watanni ukun farko na shekarar 2026, idan aka kwatanta da naira tiriliyan 2.27 da aka kashe a daidai wannan lokaci a shekarar 2025. Wannan raguwar ta kai kusan naira tiriliyan 2.18.
Masana sun danganta wannan gagarumar nasara da karuwar tace man fetur a cikin gida, musamman bayan fara aiki da fadada ayyukan matatar mai ta Dangote da sauran matatun cikin gida. Hakan ya rage dogaro da man fetur da ake shigowa da shi daga kasashen waje tare da rage bukatar kashe kudaden musayar kasashen waje.
rahoton ya nuna cewa man fetur bai ma shiga cikin manyan kayayyakin da Najeriya ta fi shigowa da su daga kasashen waje a zangon farko na shekarar 2026 ba, lamarin da ke nuna yadda tsarin samar da makamashi a kasar ke sauyawa daga dogaro da shigo da kayayyaki zuwa samar da su a gida.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa wannan ci gaba zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikin kasa, rage matsin lamba kan naira, da kuma adana kudaden shiga na kasar. Ana sa ran idan matatun cikin gida suka ci gaba da samar da isasshen man fetur, Najeriya za ta kara rage dogaro da kasashen waje wajen samar da wannan muhimmin albarkatu.
