Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta kori ma'aikatanta guda uku

Gwamnatin Kano ta kori ma’aikatanta guda uku

Date:

Majalisar dokokin Kano ta amince da korar wasu ma’aikatan hukumar lura da ayyukan majalisar dokokin (House Of Assembly Service Commision) su uku.

 

Mukaddashin gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna, ne ya aikewa majalisar sunayen mutanen uku don ta amince da korar su.

 

An samu mutanen ne da rashin gudanar da ayukan su yadda ya kamata.

Majalisa zata tantance sabbin kwamishinonin da Ganduje zai nada a ranar Litinin

 

Shugaban masu rinjaye na majalisar Labaran Abdul Madari, ya ce dokar hukumar ta baiwa gwamna dama sashi na biyar sakin layi na daya idan aka samu wani da rashin yin abinda ya dace ko laifi ya rubutowa majalisar don amincewa da sallamar su idan aka samu kaso daya bisa uku na yan majalisar.

Majalisa ta tadakatar da gina shaguna a jikin asibitin Zana a nan Kano

Ya ce za a maye gurbin wadanda aka kora da wasu da suka fito daga yankunan da suke.

 

A wani labarin kuma majalisar dokokin Kano ta ce Litinin ta makon gobe zata tantance sababbin kwamishinonin da gwamnatin jiha ta aike mata.

 

Gwamantin Kano ta aike da sunayen kwamishinonin ne domin maye gurbin wadanda suka ajiye aiki sakammakon takarar zabe a matakai daban-daban.

 

Shugaban majalisar, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya karanta sunayen sababbin kwamishinonin a zaman majalisar na Litinin din nan.

 

Cikin wadanda za a nada akwai Garba Yusuf Abubakar, tsohon kwamishinan kudi zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, da Lamin Sani Zawiyya, da Ibrahim Dan Azumi Gwarzo, da Abdul-Hamid Abdullahi Liman, da Ya’u Abdullahi ‘Yan Shana.

 

Sauran su ne, Yusif Jibril Rurum, da Adamu Abdu Fanda, da Saleh Kausani.

 

Majalisar ta kuma gayyaci mutanen takwas domin zuwa tantancesu a ranar Litinin 22 ga wannan wata na Agusta da muke ciki domin nadasu kwamishinoni a ma’aikatu daban-daban.

 

A dai zaman majalisar kungiyar tsofaffin yan majalisar dokokin ta Kano sun kaiwa majalisar ziyara tare da baiwa wasu daga cikin yan majalisar kyautuka.

 

Da yake jawabi kan makasudin ziyarar tsohon shugaban majalisar dokokin zamanin gwamnatin Malam Shekarau Balarabe Saidu Gani, ya ce sun kai ziyarar ne don nuna godiya bisa yadda majalisar ta yanzu ta tallafa musu musamman a lokacin anobar Korono.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...