Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTa’addanci: Kotu ta Daure Wadume Shekara 7

Ta’addanci: Kotu ta Daure Wadume Shekara 7

Date:

Babbar Kotun tarayya da ke  zaman ta a Abuja, ta daure kasurgumin mai garkuwa da mutane, Hamisu Bala ‘Wadume’ shekaru bakwai a gidan yari.

Mai Shari’a Binta Murtala Nyako ce ta yanke hukuncin bayan samunsa da laifi kan tuhume-tuhume 13 ciki har da mu’amala da haramtattun makamai da kuma tserewa daga gidan yari.

Haka kuma kotun ta yankewa abokanan aikata laifin nasa zaman gidan yari na shekaru uku ciki har da wani sifeton ‘yan sanda mai suna Aliyu Dadje.

Sauran sun hadar da Auwalu Bala (Omo Razor), Uba Bala ( Uba Delu), Bashir Waziri (Baba Runs), Zubairu Abdullahi (Basho) da Rayyanu Abdul.

Mai shari’a Nyako ta yanke wa Delu da Abdullahi da Abdul, hukuncin daurin shekara bakwai, yayin da ta wanke Omo Razor da Baba Runs.

Mai shari’a Nyako ta yanke wa Wadume hukunci a kan tuhume-tuhume biyu da 10 daga cikin tuhume-tuhume 13 da aka yi masa tare da wasu mutum shida.

Sojoji goma masu mukamai daban-daban da aka tuhuma a shari’ar Wadume sun hada da; Tijjani Balarabe, David Isaiah, Ibrahim Mohammed, Bartholomew Obanye, Mohammed Nura, Okorozie Gideon, Marcus Michael, Nvenaweimoeimi Akpagra, Abdullahi Adamu da Ebele Emmanuel.

 

 

Latest stories

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...

Related stories

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...