Gwamnatin Kano ta kaddamar da wani kwamiti mai ƙarfi domin binciken zargin karkatarwa, da sace kayan abincin yara masu fama da cutar yunwa wato tamowa.
Da yake kaddamar da kwamitin a yau Talata, Kwamishinan Lafiya na Kano, Dr Abubakar Labaran Yusuf, ya ce an kafa shi ne domin gano yadda aka karkatar da kayan abincin da kuma tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.
Ya ce kwamitin zai tantance adadin kayan da suka ɓace da kimar kuɗinsu.
Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da naira miliyan dari biyar wajen sayo kayan abincin domin kula da yara masu fama da matsananciyar tamowa.
Ya nuna damuwa kan yadda wasu mutane marasa kishin ƙasa ke karkatar da kayan domin sayar da su a kasuwanni, lamarin da ya hana yara masu buƙatar magani samun kulawar da ta dace.
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Aminu Bashir, ya ƙunshi mambobi goma sha takwas daga hukumomin tsaro, Majalisar Masarautu da Kwamitocin Raya Unguwanni daga yankunan Dawakin Tofa, Wudil, Rano da Bichi.
