Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya Musulmin jihar da Najeriya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 Hijiriyya, tare da kira ga mabiya addinin Musulunci da su yi koyi da darussan Hijirar ma’aiki SAW a rayuwarsu ta yau da kullum.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamna Abba ya bayyana cewa sabuwar shekarar Musulunci wata muhimmiyar dama ce ta tunawa da kyawawan halaye irin su sadaukarwa, haƙuri, jarumtaka, ladabi da kuma cikakken dogaro ga Allah a lokacin ƙalubale.
Gwamna Yusuf ya ce Hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makkah zuwa Madinah ba tafiya ce ta sauyin wuri kawai ba, illa wani babban sauyi ne da ya kafa tubalin al’umma mai adalci, tausayi da ci gaba bisa gaskiya, ’yan’uwantaka da hidima ga bil’adama.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa gwamnati za ta ci gaba da zuba jari a fannonin fannoni da suka haɗa da ilimi, lafiya, gine-ginen more rayuwa, ƙarfafa matasa da mata, noma da kuma shirye-shiryen jin daɗin al’umma domin gina Kano mai cike da ci gaba da walwala ga kowa.
