A drone view shows vessels in the Strait of Hormuz, as seen from Musandam, Oman, June 15, 2026. REUTERS/Stringer TPX IMAGES OF THE DAY
Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya sauka ƙasa da dala 80 kan kowacce ganga bayan samun kyakkyawan fata game da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran.
Farashin Brent Crude ya sauka zuwa dala 79.87 kan kowacce ganga, yayin da West Texas Intermediate na Amurka ya faɗi ƙasa da dala 77.
Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran sake buɗe mashigin Hormuz gaba ɗaya bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu.
Masana tattalin arziki sun ce saukar farashin mai na iya rage matsin hauhawar farashi a ƙasashe daban-daban, sai dai har yanzu akwai fargabar yiwuwar samun tangarɗa a bangaren samar da mai a nan gaba.
