Gwamnatin Kano ta bude kofar karbar bukatun bayar da tsirrai ga kungiyoyi da sauran al’ummar jihar, domin dasawa a unguwannin su, karkashin shirin nan na dashen bishiyoyi miliyan 10 da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.
Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Dahiru Muhammad ne ya bayyana hakan.
Hashim, ya kuma yi kira ga kungiyoyin ci gaban al’umma, da na sa-kai da na matasa, da cibiyoyin addini, makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su dasa tsirran bishiyoyi a yankunansu.
Dr Dahiru ya ce shirin dashen bishiyoyin miliyan guda 10 na daga cikin manyan manufofin gwamnatin Kano wajen yaki da kwararowar hamada, farfado da Muhallin da ya lalace, da kuma karfafa matakan kariya ga abubuwan dake da alaka da illolin sauyin yanayi yake haifarwa.
Kwamshinan ya bukaci kungiyoyi dake san shiga shirin da su gabatar da buƙatunsu ga ma’aikatar Muhalli ta Kano tare da bayanin wuraren da za su dasa bishiyoyin, yawan mambobinsu da kuma shirinsu na kula da tsirran bayan an dasa su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwamishinan na yin kira ga al’ummar Kano da su rungumi shirin a matsayin nauyin da ya rataya a wuyansu na kare muhalli.
