Gwamnatin Kano ta kaddamar da gangamin riga-kafin cutar sarke-hakora mai kama jarirai da mata masu juna biyu, domin kare rayukan al’umma musamman a yankunan karkara da ke fama da karancin ayyukan lafiya.
Da yake kaddamar da shirin, kwamishinan lafiya na Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf, ya ce Gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na ci gaba da baiwa harkokin lafiya muhimmanci musamman kula da lafiyar mata da yara da kuma yaki da cututtukan da ake iya kauce musu ta hanyar riga-kafi.
Kwamishinan ya ce za’a fara gudanar da gangamin ne daga ranar asabar 16 zuwa 20 ga watan Mayu da muke ciki a kananan hukumomi 18, inda ake sa ran za’a yiwa mata sama da miliyan 1 riga-kafin domin kare su da jariransu daga kamuwa da cutar yayin daukar ciki da haihuwa da kuma bayan haihuwa.
Dr. Yusuf ya ce gwamnati ta tanadi ma’aikatan lafiya da alluran riga-kafi da sauran kayan aiki wadatattu domin tabbatar da ganin riga-kafin ta kai ga dukkan matan da suka cancanta a cibiyoyin lafiya da cibiyoyin da aka ware domin shirin a cikin al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito kwamishinan lafiyar yana yabawa gudunmawar da kungiyoyi masu zaman kansu da masu rike da mukaman gargajiya suke bawa ma’aikatan lafiya, tare da yin kira ga mata masu juna biyu da sauran mata masu haihuwa da su fito domin karbar riga-kafin kyauta tare da rungumar kula da lafiya kafin da bayan haihuwa.
