Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Kaduna ta sanya dokar-ta-ɓaci a jihar 

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar-ta-ɓaci a jihar 

Date:

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar-ta-ɓaci a ƙananan hukumomi

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar-ta-ɓaci ta tsawon sa’o’i 24 a Ƙananan Hukumomin Jema’a da Kaura, inda ta ce tuni dokar ta fara aiki.

Sanarwar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan.

RIKICIN APC: Yadda tsagin El-Rufa’i ya tabe

Sanarwar ta ce an dauki wannan mataki ne biyo bayan shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar da kuma taimakawa jami’an tsaro don daidaita al’amura da kuma dawo da doka da oda a yankunan.

Ta kuma bayyana cewa, hukumomin tsaro na da cikakken ikon aiwatar da dokar-ta-ɓacin, inda gwamnati ta yi kira ga ɗaukacin mazauna Ƙananan Hukumomin Jema’a da Kaura da su baiwa jami’an tsaro hadin kai don dawo da zaman lafiya da bin doka da oda cikin gaggawa.

Buni ba zai sake zama shugaban APC ba-El-Rufai

Hakazalika sanarwar ta ce gwamnati ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankula da kuma duk wasu ayyukan ta’addanci da suka afku a yankin, domin za a fitar da karin bayani nan gaba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...