Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashin sojoji zuwa naira dubu 100 a wata, a wani ɓangare na ƙoƙarin inganta walwala da ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na News Central, inda ya ce duk da wannan ƙarin albashi, har yanzu akwai buƙatar ƙarin kuɗaɗe domin inganta kayan aiki da jin daɗin jami’an tsaro, musamman duba da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.
A cewarsa, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ɗaukar matakai domin inganta rayuwar sojoji da iyalansu.
Ministan ya kuma yi kira da a ƙara tsaurara hukunci kan masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata manyan laifuffuka, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage ayyukan ta’addanci da kuma ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar.
