Dakarun Operation FANSAN YAMMA na rundunar sojin kasar nan ta ce sun ceto mutum biyar daga cikin iyalan Shugaban Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Alhaji Nura Umar Abdullahi, bayan da ‘yan ta’adda suka kai hari gidansa a safiyar Asabar tare da yin garkuwa da shi.
Wadanda aka ceto sun hada da ‘ya’yansa biyu, mahaifiyarsa, matarsa da kuma wani dan uwansa.
Mai Bayar da Bayanai na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce dakarun sun isa wurin cikin gaggawa bayan jin karar harbe-harbe, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addar, lamarin da ya tilasta musu barin mutanen biyar da suka sace, yayin da suka tsere da shugaban karamar hukumar zuwa cikin daji.
Harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro uku da wani farar hula, yayin da babban dan uwan shugaban karamar hukumar ya samu raunuka.
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da aikin nema da ceto tare da bincike a wuraren da ake zargin ‘yan ta’addar ke boye.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace har sai an ceto shugaban karamar hukumar cikin koshin lafiya tare da gurfanar da wadanda suka aikata harin.
