Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Gaza, wadda ke karkashin ikon Hamas, ta ce wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya kashe shugaban ‘yan sandan arewacin yankin Falasɗinu.
Brigediya Janar Abdel-Nasser al-Maqadma, shi aka fi sani a matsayin gwamnan arewacin Zirin Gaza.
Jami’an lafiya a Gaza sun kuma ce wasu mutum uku sun mutu a wasu hare-haren da Isra’ila ta kai a daren jiya.
Har yanzu rundunar sojin Isra’ila ba ta ce komai ba game da waɗannan rahotanni.
A watan da ya gabata, Isra’ila ta kashe jami’an ‘yan sanda da dama da ke yi wa Hamas aiki, tana mai zarginsu da kasancewa barazana ga sojojinta
