Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe huɗu na yammacin Laraba, 23 ga Satumba, lokacin da fasinjojin ke tafiya daga ƙauyen Kwadige zuwa kasuwar Chai Chai sabuwa, tafkin na da nisan kilomita uku daga ƙauyen Kwadige.
Hukumar Civil defense reshen jihar Jigawa, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce bayanan farko sun nuna cewa iska mai ƙarfi na iya kasancewa sanadin kifewar kwale-kwalen.
Rahotanni sun ce manoma da ke aiki a kusa da tafkin ne suka ceto fasinjoji huɗu da suka tsira, tare da taimakon mazauna ƙauyukan Kwadige, tuni aka binne gawarwakin waɗanda suka rasa rayukansu.
Waɗanda suka rasu sun haɗa da Hasiya Mu’azu mai shekaru 13, Hauwa Lawan mai shekaru 13, Fatima Lawan mai shekaru 12 da Dawsiyya Lawan mai shekaru 13, hukumar Civil defense ta jajanta wa iyalan mamatan, tare da kira ga masu amfani da kwale-kwale da su riƙa bin matakan kariya, musamman a lokacin iska mai ƙarfi da yanayi mara kyau.
