Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa ɗalibai, malamai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, bisa zamowa zakara da jihar ta yi a jarrabawar NECO ta shekarar 2026.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran sa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Gwamna Yusuf ya ce kasancewar Kano ta sake zuwa ta daya a jere a NECO, bayan samun matsayi na farko a shekarar 2025, ya nuna cewa zuba jarin da gwamnatinsa ke yi a fannin ilimi yana haifar da sakamako me kyau.
Gwamna Abba ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa ilimi fifiko, ta hanyar ƙara kasafin kuɗi, inganta wuraren koyarwa, ɗaukar malamai da horas da su, bayar da tallafin karatu da kuma tallafawa ɗaliban da ba su da hali.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da naira biliyan 4.4 a shekarar 2026 wajen daukar nauyin ɗaliban da za su rubuta jarrabawar kammala sakandare, musamman waɗanda ba su da hali, domin rage musu nauyin kuɗaɗen karatu da jarrabawa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa zuba jarin gwamnatin bai tsaya kan ɗaukar nauyin jarrabawa ba, ya haɗa da gyaran ajujuwa, ɗaukar malamai, samar da kayan karatu da kayan makaranta, da bayar da tallafin karatu.
