Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya tsohon mai gidan sa kuma gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, murnar cika shekaru 70 da haihuwa, tare da yi masa addu’ar samun lafiya da tsawon rai.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamna Yusuf ya bayyana cikar shekarun Kwankwaso a matsayin wata muhimmiyar dama ta yin la’akari da rayuwarsa, jagorancinsa da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.
Ya kuma yaba da rawar da tsohon gwamnan ya taka wajen bunƙasa harkokin siyasa a Kano, musamman gudunmawarsa ga tafiyar da mulki, bunƙasa ababen more rayuwa da faɗaɗa shigar jama’a cikin harkokin dimokuraɗiyya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba na rokon Allah ya ƙarawa tsohon ministan tsaron, lafiya, tsawon rai, ƙarfi da juriya domin ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.
