Hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta Kano, REMASAB, da majalisar dokokin jihar, sun fara nazari da gyaran dokar da ta kafa hukumar a shekarar 2003, domin ƙarfafa ikonta na aiki, inganta tsaftar muhalli da magance ƙalubalen da ake fuskanta wajen sarrafa shara.
Taron wanda zai shafe kwanaki biyu ana gudanar da shi, zai duba yiwuwar sabunta dokar mai lamba 7 ta shekarar 2003, domin ta dace da halin da ake ciki da kuma ingantattun hanyoyin kula da muhalli na zamani.
Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan albarkatun ruwa, muhalli da sauyin yanayi na Kano, Dr Dahir Muhammad Hashim, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na duba yiwuwar sauya sunan hukumar domin ya dace da faɗaɗar ayyukan da take gudanarwa, waɗanda suka wuce kula da shara kawai.
A nasa jawabin, ɗan majalisar dokokin Kano kuma shugaban kwamitin majalisar kan muhalli, Musa Ali Kachako, ya tabbatar da cewa majalisar zata bayar da goyon bayan da ya dace domin ganin an kammala aikin gyaran dokar cikin nasara.
Shi ma da yake jawabi shugaban hukumar ta REMASAB, Dr Muhammad S. Khalil, ya ce sabunta dokar zai taimaka wajen inganta ayyukan tsaftar muhalli, tabbatar da bin ƙa’idoji, bunƙasa sake sarrafa shara da amfani da kayayyakin da za’a iya sake sarrafawa, tare da samar da sabbin damarmakin zuba jari ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu.
