Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama mutum mai suna Sallau Inuwa mai shekaru 40, bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa, mai suna Ibrahim mai shekaru 45 a unguwar Kofar Wambai dakle cikin garin Bauchi sakamakon saɓani kan kuɗin wankin mota.
Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026.
Ya ce, Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe, inda ake zargin Sallau Inuwa, wanda aka fi sani da Liman Katagum, ya daba wa Ibrahim wuƙa sau da dama kan kuɗin da ake karɓa wajen wanke kowace mota.
Sanarwar ta ce, an garzaya da Ibrahim Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Ya ce, Jami’an ’yan sanda sun fara neman wanda ake zargin, inda suka kama shi a Mararraban Liman Katagum.
Wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, yayin da Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar Bauchi ke ci gaba da bincike domin ɗaukar matakin shari’a.
