24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGanduje zai binciki badakalar kudi a jami'ar Wudil

Ganduje zai binciki badakalar kudi a jami’ar Wudil

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da kafa kwamiti da zai binciki yadda ake gudanar da al’amura a jam’ar kimiyya da fasaha da ke Wudil.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labari Malam Muhammadu Garba ya fitar ranar Talata.

Muhammadu Garba ya ce matakin ya biyo bayan takardar tuhuma da kwamitin ya rubuta bayan ziyartar jami’ar da kuma majalisar zartawa ta Kano ta yi na’am da ita.

Ya ce kwamitin zai yi duba kan dukkanin bashin da ake bin jami’ar, tare da bincikar asusun ajiyarta, sannan ya duba yadda za a dawo da kudaden da suka salwanta.

A cewar Muhammad Garba, shugaban kwamitin shi ne Babban sakataren tsare-tsare na ofishin shugaban ma’aikata na Kano.

Ragowar ‘yan kwamitin sun hadar da Babban sakataren REPA, Babban sakataren hukumar fansho, Babban sakataren ma’aikatar kudi, sai kuma Babban mai binciken kudi na jiha

Latest stories