Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBabangida ya bukaci 'yan jarida su taimakawa hadin kan kasa

Babangida ya bukaci ‘yan jarida su taimakawa hadin kan kasa

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Tsohon shugaban kasar nan Ibrahim Badamasi Babangida ya bukaci ‘yan jarida su bayar da goyon baya wajen yunkurin da ke na hadin kan kasa.

Babangida ya yi rokon ne ya yi taron manema labarai a birnin Minnan jihar Neja a wani bangare na zagayowar bikin ranar haihuwarsa.

Ya ce, idan har ‘yan jarida za suyi watsi da masu yada jita-jita, to ko shakka ba bu za su samu hanyoyin isar da sakonninsu yadda ya dace.

Ya kuma bukaci al’ummar kasar nan su ji cewa komai zai koma yadda yake kamar da, don haka kada su debe haso daga gyaruwar Najeriya.

“Ina rokonku da ku dinga hakuri da juna, kuma ku ci gaba da addu’a don neman daukin Ubangiji a game da wasu lamurra da suka shafi al’amuran rayuwa da kuma siyasa.”

Babangida ya ce akwai bukatar a ci gaba da wayar da kan jama’a a kan yadda za su zauna lafiya da juna da kuma samun ci gaba mai dorewa.

A ranar Larabar nan ne dai Baban Gida ya cike shekaru 81 da haihuwa inda kuma ya shawarci jama’a da su koma ga Allah.

Latest stories

Related stories