Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiFaduwa zabe:APC za ta gudanar da zanga-zanga a Kano

Faduwa zabe:APC za ta gudanar da zanga-zanga a Kano

Date:

Jam’iyyar APC a Jihar Kano za ta Gudanar da zanga zangar lumana domin nuna kin amincewa da sakamakon Zaben Glgwamna da ya baiwa NNPP Nasara.

Jam’iyyar APC za ta yi tattaki zuwa ofishin hukumar zabe da ke Kano a yau laraba

Tuni dai jam’iyyar ta yi watsi da sakamakon zaben gwamna da akayi wanda hukumar zabe ta bayyana cewa jam’iyyar NNPP ce tayi Nasara.

APC ta ce adadin akwatunan da aka soke yayin zaben gwamna da ya gabata zai sanya zaben amatsayin wanda bai kammala ba, wato ( inconclusive)

Hakan yasa APC za ta yi zanga zangar lumana domin nuna kin amincewa da sakamakon zaben

Dr Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC dai shi ne Wanda yayiwa APC takarar Gwamnan Kano kuma kafin wannan lokaci ya yi alkawarin amincewa da sakamakon zaben ga duk wanda Allah ya baiwa.

Yasha nanata cewa mulki na Allah ne kuma yana baiwa duk wanda yaso dan haka zai amince idan Allah ya baiwa.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...