Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa diyarsa ta taba roƙonsa da ya hada kai da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da ARISE News a ranar Litinin, inda yake magana kan yadda matasa ke sauya tunaninsu a harkokin siyasa.
A cewarsa, matasa da dama yanzu ba sa mayar da hankali sosai kan bambancin addini ko ƙabila, illa suna neman shugabanci nagari da zai magance matsalolin ƙasa.
“Har ma a zaɓen 2023, a cikin gidana, diyata tana gaya min na je na yi aiki da Peter Obi,” in ji Kwankwaso.
Tsohon gwamnan ya ce ra’ayoyin siyasar matasa sun bambanta da na tsofaffin ’yan siyasa, yana mai cewa wasu shugabanni ba su fahimci irin tasirin da matasa da kafafen sada zumunta suke da shi ba wajen sauya alkiblar siyasar Najeriya.
“Akwai shugabannin da ba su da wani kusanci da matasa maza da mata,” kamar yadda ya bayyana.
Kwankwaso ya ƙara da cewa matasa na ƙara neman shugabanni masu nagarta da za su iya magance matsalolin tattalin arziki da tsaro, maimakon siyasar addini ko ƙabila.
“Wasu na maganar addini, wasu kuma ƙabila, amma matasa suna neman shugabanci na gari ga wannan ƙasa. Kuma ina ganin suna da gaskiya,” in ji shi.
