Hukumar Zaɓe ta kasa INEC ta ce za ta tura matasa matasa masu yiwa kasa hidima na sama NYSC sama da miliyan 1.4 domin taimakawa wajen gudanar da babban zaɓen 2027.
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa babban daraktan hukumar NYSC, Olakunle Nafiu, a hedikwatar hukumar da ke Yakubu Gowon House Abuja.
A cewarsa, shirin tura yan NYSC din wani bangare ne na shirye-shiryen da hukumar ke yi tun da wuri domin tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe cikin tsari da inganci.
INEC dai na yawan amfani da mambobin NYSC a matsayin ma’aikatan wucin gadi a lokutan zaɓe, musamman wajen gudanar da ayyuka kamar rajistar masu kaɗa ƙuri’a, tantance masu zaɓe, da kuma kula da rumfunan zaɓe a sassa daban-daban na ƙasar.
